Creation Science Information & Links!
The 10 Commandments · in Hausa

   "Jehovah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce,  'Ni ne Ubangiji Jehovah-nka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.  Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.  Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.  Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Jehovah-nka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.  Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararraki da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.  Kada ka kama sunan Ubangiji Jehovah-nka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.  Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki.  Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida,  amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Jehovah-nka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku.  Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji yakeɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta  Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Jehovah-nka yake ba ka.  Kada ka yi kisankai.  Kada ka yi zina.  Kada ka yi sata.  Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.  Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa."   Exode 20:1-17


The 10 Commandments · in Hausa
http://www.creationism.org/hausa/salv10Cmd_ha.htm



Babba:  Harshen
www.creationism.org